Isa ga babban shafi
AFRIKA-ECOWAS

Mahamadou Issoufu na Nijar ya karbi jagorancin kungiyar ECOWAS

Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadou Issoufou ya karbi jagorancin kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS, yayin taron kungiyar karo na 55 da ke gudana a Abuja babban birnin Najeriya.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou RFI
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa Muhammadou Issoufou wanda shi ke jagorancin makamanciyar kungiyar ta kasashe renon Faransa tun daga shekarar 2011 ya samu goyon bayan kusan ilahirin shugabannin kasashen na ECOWAS kafin karbar jagorancin daga hannun takwaransa Muhammadu Buhari na Najeiya.

Yanzu haka dai ana ci gaba da taron na ECOWAS a Abuja, wanda ya mayar da hankali kan matsalolin tsaron da yankin ke fuskanta baya ga lalubo hanyoyin saukaka jama’a tsadar rayuwa, taron da ke samun halartar ilahirin shugabannin kasashen yankin in banda na Senegal da takwaransa na Cape Varde.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.