rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Paul Biya Ta'addanci 'Yan Aware

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jagoran adawa a Kamaru ya kubuta daga hannun 'yan aware

media
Jagoran adawar Kamaru kuma shugaban jam'iyyar SDF Ni John Fru Ndi, a Bamenda. Reinnier KAZE / AFP

Jogoran Adawa na kasar Kamaru Ni John Frundi ya samu kubuta daga hannun mayakan ‘yan awaren Ambazonia kwana daya bayan da sukayi garkuwa da shi.

 


Wannan dai shine karo na biyucikin kasa da watanni biyu da ake garkuwa da John Frundi a yankin na ‘yan aware da ake amfani da Turancin Ingilishin Kamaru.

Yayin da yake zantawa da sashin Faransancin RFI, madugun 'yan adawar ya bayyana halin da ya shiga da dalilan da yasa 'yan bindigar na 'yan aware ke garkuwa da shi.

Kalaman Ni John Frundi

“Lokacin da suka iso gidana naji wata hayaniya kafin daga bisani suyi harbi, tashi na ke da wuya kawai suka kamani suka jani a kar, nayi ta kokarin bayyana musu cewar fitana daga asibiti kenan, don su barni na sha magani na amma suka ki.

Mayakan Ambazonia da suka kaini jeji sunyi ta daukar hoto dani suna ta raira wakoki da taken Ambazonia, kuma suna rike da tutar Ambazonia.

Karo na biyu kenan suke garkuwa da ni, sun taba kama kanuwata da dan uwana, kwanaki sun kona mini mota da wani bangaren gidana.

Suna wannan ne duk wai bana mara musu baya, suna bukatan na janye ‘yan majalisun jam’iyyata SDF daga majalisar Kamaru, babu yadda na iya, sai nace musu su sake ni saboda na koma na tattauna da ‘yan majalisu na da Sanatoti na da magadan gari, don nazarin hanyar da zamu bi”.

Yanzu haka dai John Frundi ya koma gida bayan da aka sake shi daren ranar Asabar 29 ga watan Yuni.