rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Ta'addanci Najeriya Mali BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Harin ta'addanci ya hallaka Sojin Nijar 18

media
Baya ga Dakarun sojin na Nijar har 16 da harin ya hallaka, rahotanni sun ce maharan sun kuma kwashe tarin makamai REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Majiyoyin tsaro a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da wani hari da ake zargin ko dai mayakan jihadi ko kuma kungiyar Boko Haram da kai wan kan sansanin sojin kasar da ke yammaci gab da iyakar kasar da Mali tare da hallaka akalla dakarun soji 18.


Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne da yammacin jiya Litinin gab da yankin da aka hallaka Sojin na Nijar 28 cikin Mayu.

Farmakin kan Sojin na Nijar shaidun gani da Ido sun ce, maharan sun isa sansanin ne a ayarin motoci tare da babura rike da muggan makamai a gab da yankin Tongo-Tongo tare da yiwa Sojin kawanya.

Haka zalika wasu na ganin harin na a matsayin daukar fansa kan harin watan jiya da sojin na Nijar tare da hadin gwiwar takwarorinsu na Amurka da Faransa suka kai tare da hallaka mayaka masu ikirarin jihadi 18 cikin watan jiya.

Harin na yammacin jiya Litinin na zuwa ne dai dai lokacin da kasar ta Nijar ta fara karbar bakon taron nahiyar Afrika kuma yankin da aka kai harin da wajen da taron ke gudana na da tazarar kilomita 200 ne kacal.

Baya ga kisan sojojin na Nijar har 16 wasu bayanai na nuni da cewa maharan sun kuma yi awongaba da tarin motoci da makamai.