Mutane dubu 1 sun halaka a sabon yakin Libya
Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, ya bukaci tsagaita wutar yakin da ake fafatwa a Libya, tsakanin sojin gwamnatin Fayez Al-Sarraj da kasashen duniya ke marawa baya, da dakarun Janar Khalifa Haftar mai rike da yankin gabashin kasar.
Wallafawa ranar:
Kiran na majalisar dinkin duniya ya zo ne bayan da adadin mutane dubu daya suka halaka, a dalilin sabon yakin da aka shafe watanni uku ana gwabzawa, a kokarin da Haftar ke yin a kwace iko da birnin Tripoli, hedikwatar gwamnatin ta Libya.
Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar, ya nuna cewa, akalla mutane dubu 5 yakin ya jikkata, wasu sama da dubu 100 kuma suka tsere daga muhallansu, bayaga bayaga hasarar rayuka dubu guda.
A ranar talata, 2 ga watan Yuli, wani farmakin jiragen yaki kan sansanin Tajoura dake birnin Tripoli, ya halaka 'yan gudun hijira 53, wanda tuni gwamnatin Al-Sarraj ta dora alhakin kan dakarun Janar Haftar, zargin da ya musanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu