rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Nijar Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya da Benin sun sanya hannu a yarjejeniyar kasuwancin bai daya

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya ke sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwancin bai daya tsakanin kasashen Afrika a birnin Niamey na Nijar Nigeria Presidency/Handout via Reuters

Kasashen Najeriya da Jamhuriyar Benin sun amince da sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwancin bai daya tsakanin kasashen Nahiyar Afrika matakin da ya mayar da adadin kasashen da suka amince da yarjejeniyar zuwa 54 daga cikin kasashen Nahiyar 55.


Shugaba Muhammadu Buhari da takwaransa Patrice Talon sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ne yayin taron tsakiyar shekara na kungiyar Tarayyar Afrika da ke gudana can a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.

Yayin taron ne dai za a kaddamar da kasuwar ta bai daya wadda za ta zamo irinta ta farko a duniya ga mutane biliyan 1 da miliyan 200.

Yanzu haka dai kasar Eritrea ce kadai ta rage a jerin kasashen Afrika da ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar.