Isa ga babban shafi
Wasanni

CAF ta musanta bincikar Zimbabwe da Congo kan zargin almundahana

Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF, ta musanta cewa tana bincike kan zargin da ake yiwa Zimbabwe da Jamhuriyar Congo na aikata almundahanar shirya wasan da suka fafata a matakin rukuni na gasar cin kofin kasashen Afrika da ke gudana a Masar, wanda Zimbabwe ta sha kaye da 4-0.

Mouad Hajji Babban sakataren hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF.
Mouad Hajji Babban sakataren hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF. HuffPost Maghreb
Talla

Babban sakataren hukumar ta CAF, Mouad Hajji, yace a iyaka saninsa, har yanzu babu wanda ya gabatar musu da korafi kan zargin sahihancin wasan na ranar 30 ga watan Yuni, duk da cewa a makon da ya gabata, kafafen yada labarai da dama sun rawaito labarin.

Jaridar Herald da ke Zimbabwe ce ta soma wallafa labarin da ke cewa attajirin Jamhuriyar Congo kuma dan siyasa, Moise Katumbi, ya bi ta bayan fage wajen bawa mai tsaron ragar Zimbabwe Elvis Chipezeze toshiyar baki, domin baiwa yan wasan Jamhuriyar Congo damar samun nasara a kansu.

Rahoton na jaridar Herald ya kuma ce, idan CAF ta samu Jamhuriyar Congo da laifi, za ta kori kasar daga gasar ta bana, ta kuma haramta mata sake shigarta na tsawon shekaru 3, da kuma tilasta mata biyan tara mai ciwo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.