Isa ga babban shafi
Senegal

Jami'an tsaron Senegal sun kame 'yan aware 13

Jami’an tsaron kasar Senegal sun kama wasu ‘yan aware 13 da ke halartar wani haramtaccen taro a Yankin Casamance da ke neman ballewa daga kasar.

Yankin Karang da ke kan iyakar Senegal da Gambia.
Yankin Karang da ke kan iyakar Senegal da Gambia. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Kakakin sojin Senegal yace ana tsare da mutanen ne a garin Kagnobon da ke kusa da iyakar Gambia.

Majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar mutanen 13, na daga cikin ‘ya’yan kungiyar Casamance Movement of Democratic Forces MFDC da ke karkashin Salif Sadio.

A ranar 22 ga watan Yuni, gwamnatin Senegal ta haramtawa magoya bayan Salif Sadio gudanar da kowane irin taro.

Cikin shekarar 1982 kungiyar mayakan sa kai ta MFDC ta soma gwagwarmayar neman ‘yancin kudancin kasar Senegal, da ke yankin kudu da kasar Gambia, amma bayan da Shugaba Macky Sall ya dare shugabancin Senagal a 2012, aka soma tattaunawar sulhu tsakanin mayakan da gwamnati a shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.