rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Afrika Kwallon Kafa Uganda Senegal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kocin Uganda ya rasa aikinsa

media
Kocin kasar Uganda da ya rasa aikinsa Sebestian Desabre. Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta Uganda ta kori kocin tawagar yan wasan kasar Sebestian Desabre, sakamakon ficewarsu daga gasar cin kofin Afirka a zagaye na biyu.


A jiya lahadi, kwanaki biyu, bayan rashin nasarar da suka yi a hannun Senegal da 1-0, hukumar kwallon ta Uganda FUFA ta bayyana korar kocin.

A watan Disamba na shekarar 2017, Desabre mai shekaru 42, ya soma horar da yan wasan Uganda.

Kocin na Uganda shi ne mai horaswa na biyu da aka kora a gasar cin kofin Afrika ta bana, bayan Javier Aguirre na Masar da hukumar kwallon kasar ta sallama a ranar asabar, bayan rashin nasararsu a hannun Afirka ta kudu.