Isa ga babban shafi
Faransa-Najeriya

Macron zai gana takwarorinsa na Ghana da Ivory Coast

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai karbi bakuncin takwarorinsa na kasashen Ghana da Ivory Coast a ranakun Talata da Alhamis a birnin Paris.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da uwargidansa Brigitte Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da uwargidansa Brigitte Macron. AFP / Mandel Ngan
Talla

Sanarwa gwammatin Faransa tace shugaba Macron zai fara ne da karbar bakuncin shugaban Ivory Cost Alassan Ouattara a ranar Talata, daga bisani kuma ya gana da shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana a ranar Alhamis.

Sai dai sanarwar ba ta yi Karin bayani kan batutuwan da shugabannin za su tattauna a kai ba.

Yayin ziyarar shugaban Ghana Akufo Addo zai halarci taron kasuwanci tsakanin kasashen biyu a ma’aikatar harkokin kasuwanci da tattali ta Faransa.

A yayin ziyararsa kasashen Afrika a watan Disamban 2017, Emmanuel Macron yayi zazzafar muhawara da daliban jami’ar Ouagadougo da ke Burkina Faso dangane da manufofin Faransa kan kasashen Afirka.

Macron yayi jawabin karshe na karkare ziyarar nahiyar ta Afrika a kasar Ghana, inda ya bukaci kasashen Afirka su maida hankali wajen dogaro da kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.