rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha Daular Larabawa Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Habasha za ta aike da 'yan kasar dubu 50 zuwa Daular Larabawa

media
Fira ministan Habasha Abiy Ahmed. AFP/Monirul BHUIYAN

Habasha tace za ta tura ‘yan kasar 50,000 zuwa Daular Larabawa domin gudanar da aikace aikace a kasar.


Fira ministan Habasha Abiy Ahmed ya bayyana haka yayin da yake jawabi a zauren Majalisa, inda ya ce matakin yunkuri ne na tura ‘yan kasar da suka kware a fannoni daban daban kasashen duniya domin yin aiki.

Ahmed yace a karkashin yarjejeniyar da suka kulla da Daular Larabawa, Habasha za ta aike da ma’aikatan dubu 50 ne tsakanin wannan shekarar zuwa 2020, yayin da kuma za ta aike da Karin wasu 200,000 nan da shekaru 3 masu zuwa.

Fira ministan yace suna tattaunawa da kasashen Japan da wasu kasashen Turai domin kulla irin wannan yarjejeniya.