Isa ga babban shafi
AFRIKA-ECOWAS

Takaddar kudin ECO za ta kankama a shekarar 2020- Ouattara

Shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya ce kasashen da ke Afirka ta Yamma da suka cika sharadodin samar da kudin bai daya da aka yi wa suna ECO za su aiwatar da shirin a shekara mai zuwa ta 2020.

Yanzu haka dai shugabannin kasashen na yammacin Afrika sun amince da kankamar shirin nan da shekarar 2020.
Yanzu haka dai shugabannin kasashen na yammacin Afrika sun amince da kankamar shirin nan da shekarar 2020. AFP Photo/ISSOUF SANOGO
Talla

Shirin samar da kudin bai dayan ya samo assali shekaru sama da 30 da suka gabata, amma aka kasa samun biyan bukata saboda banbance babancen da ke tsakanin kasashen kungiyar ECOWAS.

A watan jiya shugabannin su ka amince da shirin, yayin da shugaba Ouattara ya ce Cote d’Ivoire na goyan bayan sa dari bisa dari.

Ana saran tsarin kudin ya taka muhimmiyar rawa wajen hade kan kasashen baya ga bunkasa tattalin arzikinsu da kuma samar da ayyukan yi.

Kasashen na yammacin Afrika dai yayin taron Kungiyar AU na tsakiyar shekara da ya gudana a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, sun amince da sanyawa kudin suna ECO wanda zai zamo takaddar kudin da ilahirin kasashen yammacin na Afrika za su rika amfani da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.