rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres Mozambique

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taimakon dala miliyan 273 ga Muzambique ya yi kadan-Guterres

media
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres tare da shugaban kasar Mozambique FIilipe Nyusi ANTONIO SILVA / LUSA

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewar adadin kudaden agajin da kasashen duniya suka yiwa Mozambique sakamakon bala’in ruwa da iska da ya afka mata sun gaza abinda kasar ke bukata.


Kungiyoyin agaji na duniya sun yi alkawarin baiwa Mozambique tallafin Dala sama ad biliyan guda ne domin shawo kan bala’in ruwa da iskar da suka afkawa kasar har sau biyu cikin mako guda, amma Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewar abinda kasar ke bukata ya zarce Dala biliyan 3 domin dawo da kasar cikin hayyacin ta.

Tun farko dai an tara Dala miliyan 273 wajen gidauniyar gaggawan da aka tarawa kasar.

Sakatare Janar Antonio Guterres dake ziyarar gani da ido a kasar, yace agajin kudaden da aka tara na gaagwa da kuma sake gina kasar sun gaza abinda ake bukata.

Guterres ya jaddada cewar, wannan bala’i da ya samu Mozambique nada nasaba da sauyin yanayi, kuma Mozambique bata daukar wani mataki ko kankani wajen haifar da matsalar, amma kuma ga shit ana fuskantar radadin sa.

Sakataren ywanda ya gana da shugaban kasa Filipe Nyusi yace ya zama wajibi ga kasashen duniya su kaiwa kasar dauki.