rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zamfara

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan bindigar da suka tuba sun soma mika makamansu

media
Shirin afuwa ya rage hare-haren yan bindiga a Zamfara. Jakarta Globe

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara a Najeriya, Usman Nagoggo, yace ‘yan bindigar da suka tuba sun soma mika makamansu ga gwamnati.


Nagoggo, ya bukaci sauran yan bindigar da su fito don mika nasu makaman ba tare da fargabar fuskantar tsangwama ba, domin ya baiwa dukkan masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro a yankin umarnin dakatar da daukar mataki kansu, ko da kuwa, an gansu suna zirga-zirga a babura, ko kuma gudanar da taro.

Kwamishinan yan sandan ya kara da cewa, shirin sulhu tsakaninsu da yan bindiga, ya taimaka matuka wajen rage tashin hankali da jama’a ke fuskanta na yawaitar hare-hare, biyo bayan taron ganawa tsakaninsu da sauran jami’an tsaron sa kai, a karshin jagorancin gwamnati da sarakunan gargajiya.

A karshen watan Yuni da ya gabata 'yan bindiga a jihar Zamfara suka gindaya sharuddan da suka ce idan aka cika za su ajiye makamansu.

Cikin sharuddan da yan bindigar suka gindaya a waccan lokacin kuma akwai daina kashe wadanda ake zargi a kasuwannin kauye da wasu jami’an tsaron sa kai ke yi a sassan jihar, zalika yan bindigar sun bukaci basu damar halartar kasuwanni ba tare da tsangwama ba.