Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Wasikar Obasanjo ta zargi Buhari da ingiza Najeriya cikin hadari

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya sake aikewa shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari da wasika wadda ke gargadinsa kan tsanantar matsalar tsaro da kabulanci da Najeriyar ke fuskanta inda ya ce Buharin kadai ke da zarafin iya dakile matsalar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo nationaldailyng.com
Talla

Zungureriyar wasikar wadda ke dauke da kwanan watan yau, 15 ga watan Yulin shekarar 2019, tsohon shugaban na Najeriya Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa tashe-tashen hankula baya ga tsanantar rikicin kabilanci ya hauhawa ne tun bayan hawan shugaban mai ci mulki a shekarar 2015.

A cewar wasikar ta Obasanjo wanda ya mulki kasar wa’adi 2 a shekarun 1999 da kuma shekarar 2007 rarrabuwar kai tsakanin mabanbantan kabilu da aka daina gani tsawon shekaru a Najeriyar yanzu ta dawo sabuwa indakai tsaye ya zargi gwamnatin da kuma jami’an tsaronta kan rawar da su ke takawa.

A cewar wasikar ta Obasanjo, wadda ba ita ce karon farko da yak e aikewa shugaban mai ci tare da sukar salon kamun ludayinsa ba, ya ce hanya daya ta magance matsalar da kasar ta fada, dole ne Muhammadu Buhari ya ajje dabi’ar nuna kyama ko banbanci kokuma kiyayya ga wasu kabilu a kasar.

A cewar Olusegun Obasanjo, yanzu haka wasu kasashen yammacin duniya sun fara gargadin yiwuwar tsundumar Najeriyar cikin tsananin rikicin kabilanci wanda Olusegun Obasanjo kai tsaye ya dora laifin kan shugaba Muhammadu Buhari.

Olusegun Obasanjo cikin wasikar ta shi ya bayyana cewa akwai bukatar ‘yan bindigar da ake alakantawa da makiyaya kai tsaye su fito su bayyana bukatunsu, don su zauna da gwamnati da nufin magance matsalar, maimakon fadada ayyukansu na ta’addanci a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.