Isa ga babban shafi
Mali

Gwamnatin Mali ta yi watsi da tayin shiga tattaunawa da 'yan ta'adda

Ministan harkokin wajen Mali, Tiébilé Dramé, ya yi watsi da batun shiga tattaunawa da mayakan masu ikararin jihadi a kasar, da suka hada da na yankin tsakiyar kasar, da tashe tashen hankula suka dabaibaye.

Wasu sojin Faransa a kasar Mali.
Wasu sojin Faransa a kasar Mali. REUTERS/Joe Penney
Talla

Ministan ya bayyana haka ne yayin zantawa da kamfanin dillancin labara na AFP a ranar litinin.

Da aka tambaye shi kan wani rahoto da cibiyar nan mai nazari kan rikice rikice a duniya International Crisis Group (ICG) da ta bada shawarar shiga tattaunawa da mayakan na jihadi, musamman shugabanin, "Katiba na Macina" da mai waázin nan Amadou Koufa, da ya bulla a 2015 a yankin tsakiyar kasar ta Mali, Tiébilé Dramé ya bayyana cewa wannan ba matsayin gwamnati bane

Inda ya kara da cewa matsayar da suka dauka ita ce ta makwabtan kasar a karkashin gungun G5 Sahel kuma babu matsayin shiga tattaunawa da ‘yan taádda halin yanzu a gabansu.

Wata muhawarar samun fahimtar juna da aka gabatar a shekarar 2017 a Mali, ta bukaci shiga tattaunawa da Iyad Ag Ghaly da kungiyarsa ke da alaka da Al’Qaeda da Kungiyar da malamin nan mai waázi bafullace Amadou Koufa. Amma duk gwamnatin Mali da Faransa suka yi watsi da shawarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.