rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ya bukaci a gaggauta fara biyan sabon albashi na naira dubu 30

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP/SAUL LOEB

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin gaggauta fara biyan ma’aikatan kasar dake karbar kasa da naira 30,000 sabon albashi. A watan janairu shekarar 2019,Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da wani sabon kwamiti da zai yi nazari kan ma’aikatan da ke karbar albashi mai tsoka fiye da ka’ida, da kuma zaftare albashin duk wanda aka samu akan tsarin.


Shugaban hukumar kula da albashin ma’aikatan gwamnati, Dr Richard Onwuka Egbule ya bayyana matakin wanda yace zai fara aiki daga 18 ga watan Afrilun da ya gabata.

Jami’in yace karin albashin ya shafi masu karbar kasa da naira 30,000 ne kawai.

A farkon shekarar bana ne majalisar kolin Najeriya da ta kunshi shugaban kasa da tsaffin shugabannin kasa da Gwamnonin Jihohi da kuma babban alkalin kasa mai ci da wadanda suka yi ritaya ta amince da naira dubu 27 a matsayin albashi mafi karanci a Jihohi, yayin da ma’aikatan tarayya kuma za su karbi naira dubu 30.