rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mawaka Afrika ta kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Fitaccen mawakin Afrika ta kudu Johnny Clegg ya rasu

media
Fitaccen mawakin Afrika ta kudu marigayi Johnny Clegg © RFI/Edmond Sadaka

Daya daga cikin fitatatun mawakan Afrika ta kudu, Johnny Clegg ya mutu yana da shekaru 66 a Afrika ta kudu kamar yadda Manajan sa Roddy Quinn ya sanar.


Manajan yace mawakin ya rasu ne lokacin da iyalan sa ke kewaye da shi, bayan ya kwashe sama da shekaru 4 yana fama da cutar kan sa.

Mawakin da aka yiwa lakabi da ‘White Zulu’,bature dake zaune da yan kabilar Zulu ya kware wajen hada wakar zamani da na al’adar Zulu, abinda ya sa shi fice a duniya.

Daya daga cikin wakokinsa da suka yi fice sun hada da wakar da yayiwa tsohon Shugaban Afrika ta Kudu marigayi Nelson Mandela a lokacin da yake kargame.

Mahaifinsa dan kasar Birtaniya, yayinda mahaifiyar sa yar Zimbabwe,Johnny Clegg ya samu isowa Afrika ta kudu ya na mai shekaru bakwai a Duniya, kuma tarihi ya nuna cewa marigayi Johnny Clegg yayi suna a wajen kasar fiye da Afrika ta kudu,