Isa ga babban shafi
Duniya

Mutane biliyan 2 a duniya na fama da rashin abinci mai inganci

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane biliyan 2 ne a duniya ba sa iya samun abinci mai inganci, lamarin da ke sanya su cikin hadarin kamuwa da cutuka, kuma mafi yawan su na zaune ne a nahiyoyin Arewacin Amurka da Turai.

Rashin abinci  na daya daga cikin matsallolin da ya hadabi jama'a a Duniya
Rashin abinci na daya daga cikin matsallolin da ya hadabi jama'a a Duniya Pixabay
Talla

Rahoton hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da abinci da wadatuwarsa, na 2019 ya ce a halin da ake ciki, fiye da kashi daya bisa hudu na al’ummar Duniya da kyar da jibin goshi suke cin abinci.

Adadi ya kunshi kashi 8 na jama’ar da ke Turai da arewacin Amurka, wadanda a karon farko suka tsinci kansu cikin matsalar wadataccen abinci mai inganci da ma yunwa kai tsaye.

Karancin abinci mai inganci ya shafi mutane ne da ya zame wa dole su rage ingancin abin da suke ci sakamakon rashin kudi da sauran matsaloli, wadda hakan ka iya sanadin muguwar kiba,lallurar da ke shafar bunkasa jiki da kwakwalwar yara.

Wannan sabon rahoton ya yi nuni da cewa akwai mutane da ke fama da muguwar kiba a duniya a yanzu fiye wadanda ke fama da yunwa, kuma nau’ukan abincin da suke ci ne silar haka, amma kuma ya bayyana cewa adadin masu fama da yunwa a duniya ya karu a shekarar 2018, sannan yunwa takaru a nahiyar Afirka da Gabas Ta Tsakiya, Latin Amurka da yankin Caribean kuma ya daura alhakin haka ne kan rikice rikice da sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.