Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugabannin kudanci da tsakiyar Najeriya sun musanta korar Fulani

Kungiyar shugabannin ‘yan kudancin Najeriya da na Middle Belt sun bayyana cewa ko da wasa basu taba cewa Fulani makiyaya su bar yankunan su ba, kamar yadda Dattawan Arewacin Najeriya suka basu umurnin komawa gida.

Wani filin kiwo a yankin jihar Kaduna da ke Najeriya.
Wani filin kiwo a yankin jihar Kaduna da ke Najeriya. STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images
Talla

Sanarwar da kungiyar ta raba wa manema labarai, mai dauke da sanya hannun Chief Edwin Clark da Chief Ayo Adebanjo da Chief John Nwodo da kuma Dr Pogu Bitrus sakamakon kiran da Dattawa da Matasan Arewa suka yi cewar, Fulani su koma Arewa, ta bayyana damuwa da rahotan kiran da shugaban Yan Arewa Farfesa Ango Abdullahi ya yiwa Fulanin cewa su koma yankin su.

Sanarwar ta ce shugabannin Yan kudancin Najeriyar da Middle Belt basu da matsala da Fulani makiyaya, saboda sun dade suna zama tare da su kuma su na gudanar da ayyukan su ba tare da matsala ba.

Kungiyar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya taka wa Farfesa Ango Abdullahi da mukarraban sa birki kan abinda suka kira kalaman da kan iya haifar da yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.