rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa Rashawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ramaphosa na Afrika ta kudu na fuskantar tuhumar rashawa

media
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa Delwyn.verasany.jpg

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Afirka ta kudu ta zargi shugaba Cyril Ramaphosa da yiwa Majalisa karya dangane da taimakon Dala 36,000 da wani kamfani ya baiwa gidauniyar yakin neman zaben sa bara.


Shugabar hukumar Busisiwe Mkhwebane tace binciken da ta gudanar ya nuna cewar shugaban ya baiwa majalisar bayanan karya lokacin da yake amsa tambayoyi kan kudin a watan Oktoban shekarar 2017.

Lokacin da Majalisa ta bankado maganar, Ramaphosa ya ce taimako ne ga dan sa, amma kuma daha bisani yace taimako ne domin yunkurin san a zama shugaban ANC.