Isa ga babban shafi
Gambia

Sojan Gambia ya dora alhakin kisan sanannen dan jarida kan Jammeh

Wani sojan Gambia ya dora alhakin kisan sanannen dan jaridar kasar Deyda Hydra da aka halaka a shekarar 2004, kan tsohon shugaba Yahya Jammeh.

Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh.
Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh. REUTERS/Carlos Garcia Rawlins/Files
Talla

Yayin bayani gaban kwamitin da ke bincikar tsohuwar gwamnatin Jammeh, Laftanar Malick Jatta ya ce yana daga cikin wadanda suka aiwatar da kisan gillar.

Baya ga dora alhakin kisan gillar kan tsohon shugaba Yahya Jammeh, Laftanar Malick Jatta ya kuma bayyana wasu sojojin da suka hada da Captain Tumbul Tamba, Alieu Jen, da kuma Sana Manjang a matsayin wadanda suka halaka dan jaridar tare.

Deyda Hydara babban edita ne na jaridar The Point daily wadda ya taimaka wajen kafuwarta a Gambia, zalika wakili ne na kamfanin dillancin labarai na AFP da kuma kungiyar ‘yan jaridu ta duniya RSF.

A watan Disamba na shekarar 2004 ‘yan bindiga suka harbe Hydara har lahira cikin motarsa a wajen birnin Banjul, kisan da duniya tayi tur da shi a matsayin daya daga cikin shaidun mulkin kama karya na tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh.

Yayin bada nashi bahasin gaban kwamitin bincikar tsohuwar gwamnatin kasar, abokin aikin Hydara, Pap Babucar Saine, yace an halaka abokin nasa ne saboda rahotannin da ya wallafa kan zargin tsohon shugaban da laifukan cin hanci da rashawa.

A shekarar 2017, kungiyoyin fararen hula da kuma iyalan wadanda gwamnatin Jammeh ta ci zarafi, ciki harda dan Deyda Hydara, suka soma fafutukar ganin an bi musu hakkinsu, da kuma hukunta tsohon shugaban na kasar Gambia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.