Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta fice daga sabuwar gasar kwallon kwandon Afrika

Algeria ta fitar da Najeriya daga sabuwar gasar kwallon Kwando ta nahiyar Afrika da kasashe ke halarta da tawagogin ‘yan wasansu da ke kungiyoyin cikin gida, da kasar Mali ke karbar bakunci.

Algeria ta doke Najeriya da 85-80 a sabuwar gasar kwallon kwando ta nahiyar Afrika.
Algeria ta doke Najeriya da 85-80 a sabuwar gasar kwallon kwando ta nahiyar Afrika. REUTERS/Ivan Alvarado
Talla

Tawagar kwallon kwandon Najeriya ta D ‘Tigers ta sha kashi ne a hannun takwararta ta Algeria da 85 -80.

A halin yanzu Algeria za ta fafata ne da kasar Angola a zagayen daf da na kusa da karshe.

Wannan dai shi ne karo na farko da ake gudanar da sabuwar gasar kwallon kwandon ta AfroCan a karkashin hadin gwiwar jagorancin hukumar kula da wasannin kwallon kwandon ta duniya FIBA da kuma takwararta ta nahiyar Afrika.

Za a rika buga sabuwar gasar ta AfroCan duk bayan shekaru 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.