Isa ga babban shafi
Afrika

Kasashen Afrika na fama da bala'in fari

Kungiyoyin Agaji sun yi gargadin cewar kasashen da ke Gabashin Afirka da suka hada da Somalia da Kenya da kuma Habasha na fuskantar fari wanda ya yi kama da irin wanda aka gani a shekarar 2011 da ya haifar da yunwar da ta kashe dubban mutane.

Akalla mutane dubu 260 sun rasa rayukansu sakamakon fari a shekarar 2011.
Akalla mutane dubu 260 sun rasa rayukansu sakamakon fari a shekarar 2011. DeAgostini/Getty
Talla

Kungiyar Agaji ta Oxfam ta ce yanzu haka akalla mutane sama da miliyan 15 ke fafututar samun abinda za su ci da ruwan sha sakamakon parin da aka samu wanda ya lalata amfanin gona da kona tafkuna.

Daraktar Shiyar Gabashin Afrika ta Kungiyar, Lydia Zigomo ta ce bai dace ace duniya ta zuba ido har sai an ga abinda ya faru a shekarun baya, yadda ungulaye ke cin naman matattun mutane ta kafar talabijin kafin daukar mataki akai ba.

A shekarar 2011 akalla mutane sama da 260,000 suka mutu sakamakon fari da kuma yaki, kafin duniya ta farga.

Kungiyar ta bukaci kungiyoyin kasashen duniya da masu bada agaji da su taimaka domin ceto rayukan masu fuskantar bala’in farin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.