rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Boren Fursunoni a Kamaru ya jikkata mutane 43

media
Wani bangare na gidan yarin birnin Yaounde a Kamaru REUTERS/Stringer

Akalla Fursunoni 43 sun jikkata yayin wani bore da ya barke a ranar Talatar da ta gabata a gidan yarin Bueya, babban birnin yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru, daya daga cikin yankuna biyu dake amfani da turancin Inglishi, inda sojojin gwamnati da na ‘yan aware ke ci gaba da fada kusan shekaru 3, kamar yadda wata majiyar gwamnatin kasar ta sanar.


Cikin bayanan da gwamnatin Kamaru ta fitar game da rikicin Fursunonin wadanda galibi ‘yan aware ne, ta ce akwai jami’an tsaronta 2 da suka jikkata lokacin da suke kokarin kwantar da hankali sakamakon fara boren.

A cewar ministan sadarwa na Kamaru René Emmanuel Sadi yanzu haka wadanda suka jikkata yayin boren na ci gaba da karbar kulawa a asibitin kurkukun wadanda jikinsu ya tsanata kuma aka fitar da su asibitin wajen gari don ceto rayukansu.

Ministan wanda ke cewa, babu asarar rayuka yayin hatsaniyar ta ranar Talata, ya ce akwai yara kanana 20 a cikin rikicin wadanda ake tsare da su bayan samunsu da hannu a wata hatsaniya a yankin ‘yan aware, wadanda yanzu haka aka mika kulawarsu karkashin yan sandan maáikatar sharaá da ke gudanar da bincike a kansu.

Wasu majiyoyi mabanbanta sun bayyana cewa Fursunonin sun shiga boren ne, bisa bukatar son gwamnati ta inganta yanayin da ake tsare dasu a gidajen yarin, tare da ganin an gudanar da yi masu sharaá kan lokaci bisa kuma adalci.

idan dai ba a manta ba ko a cikin daren litanin zuwa safiyar talatar da suka gabata, fursunonin yan asalin yankin yan awaren mai amfani da Iglishi a Kamaru sun gudanar da wani bore a babban gidan yarin Yaoundé wanda ya tilastawa jamián tsaro buda wuta, da yak ai ga jikkatar fursunoni 2.