rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar Shi'a

media
Wasu mambobin kungiyar Shi'a a Najeriya lokacin da su ke zanga-zangar neman ganin an saki shugabansu Ibrahim Zakzaky AFP PHOTO PIUS UTOMI EKPEI

Gwamnatin Najeriya ta sanar da haramta kungiyar Shi’a sakamakon zanga zanga da arangamar da ake cigaba da samu tsakanin mambobinta da jami'an tsaro a Abuja babban birnin kasar.


Mai shari’a Nkeonye Maha ta bada umurnin, inda ta danganta duk wani taro ko ayyukan da kungiyar za ta yi a Najeriya a matsayin haramtacce da kuma ta’addanci.

Mai shari’ar ta kuma haramta duk wani dan kungiyar ko kuma jama’a shiga wata hulda da ta shafi kungiyar ta kowacce fuska a Najeriya.

Sai dai kungiyar ta yi watsi da matakin da kotun ta dauka wanda ta ce ya sabawa dokar kasa.

Mai Magana da yawun ta, Abdullahi Musa ya ce kungiyar ba ta da rajista saboda kungiyar addini ce, kuma kotun ba ta da hurumin hana su gudanar da ayyukan su.