rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

BOKO HARAM Najeriya Maiduguri

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Boko Haram ta kashe masu sallar Jana'iza 65 a Maiduguri

media
Jagoran kungiyar Boko Haram a Najeriya Abubakar Shekau © AFP PHOTO / BOKO HARAM

Rahotanni daga Najeriya, sun bayyana cewa mayakan Boko Haram sun hallaka akalla mutane 65 da ke tsaka da sallar gawa a yankin Nganzai da ke gab da birnin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.


Wani jami’in tsaron sa kai da aka bayyana sunansa da Bunu Bukar, ya tabbatar da misalign karfe 10 na safe lokacin da al’umma ke dawowa daga kauyen Goni Abachari zuwa Badu Kuluwa ne kwatsam mayakan na Boko haram akan babura suka bude wuta kansu tare da hallaka mutane 65.

A cewar mahukuntan yankin adadin mutanen da Boko Haram ta hallaka a harin ka iya karuwa bayan raunatar mutane da dama.