Isa ga babban shafi
Sudan

An takaita zirga-zirga a Sudan saboda kashe bore

Hukumomi a Sudan sun kafa dokar takaita zirga–zirga cikin dare a garuruwa hudu na jihar Kordofan da ke arewacin kasar da suka hada da babban birnin jihar, Al–Obeid, sakamakon harbe wasu masu zanga–zanga biyar har lahira a  yayin gudanar da wani gangami.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Sudan
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Sudan REUTERS/Stringer
Talla

Wata sanarwa daga Ofishin Gwamnan Jihar Kurdofan ta ce, dokar za ta fara aiki ne daga karfe tara na dare zuwa karfe shida na safe har zuwa wani lokaci da ba a fayyace ba.

Masu zanga–zanga biyar, ciki har da dalibai, aka harbe har lahira a ranar Litinin , kwana guda gabanin tattaunawar lalubo mafita kan batun samar da gwamnatin farar hula tsakanin shugabannin masu zanga–zangar da janar–janar na soji masu jan ragamar mulkin kasar.

Tuni dai bangarorin biyu suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar raba mukamai da zummar kafa gwamnatin hadin-gwiwa da za ta kunshi farar hula da sojoji, wadda daga bisani  za ta kai ga kafa gwamantin farar hula zalla.

Wani kwamitin likitoci da ke da alaka da zanga-zagar ya tabbatar da shahadar wadannan mutane biyar, inda ya ce, sun mutu ne sakamakon raunukan da suka samu daga harsashen bindigar kwararrun masu kyare a yayin zanga–zangar da suka ce ta lumana ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.