rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Nijar Chadi Kamaru BOKO HARAM Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojojin hadin gwiwa sun dakile harin Boko Haram

media
Wasu dakarun sojin Najeriya. AFP

Rundunar hadin gwiwa ta kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi, tayi nasarar dakile wani hari da mayakan kungiyar Boko haram ta yi yunkurin kaiwa a Baga.


Mai Magana da yawun rundunar, Kanal Timothy Antigha yace mayakan sun yi kokarin tafka barnar ce da misalin karfe 5.30 na asuba, inda dakarun dake aiki a garin suka murkushe su.

Kanal Antigha ya ce dakarun hadin gwiwar sun samu nasarar halaka 10 daga cikin mayakan na Boko Haram, daga cikinsu kuma harda ‘yan kunar bakin guda 4.

Yunkunrin farmakin na baya bayan nan, ya zo ne kasa da mako daya, bayan da mayakan na Boko Haram suka halaka sama da mutane 60 yayinda suke gudanar da jana’iza a Jihar Borno.