Isa ga babban shafi
Congo-Ebola

Ebola ta hallaka mutum na 2 a birnin Goma na Jamhuriyar Congo

Mahukuntan kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sun tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cikin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a garin Goma kwanakin kalilan bayan mutuwar mutum na farko a cikin watan nan.

Mahukunta a Congo sun bayyana cewa babu alaka tsakanin mutum na farko da na biyun da suka mutu a birnin na Goma sanadiyyar cutar ta Ebola
Mahukunta a Congo sun bayyana cewa babu alaka tsakanin mutum na farko da na biyun da suka mutu a birnin na Goma sanadiyyar cutar ta Ebola REUTERS/James Akena
Talla

Wata majiya daga fadar shugaban kasar ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ta tabbatar da cewa da safiyar yau ne aka wayi gari da mutuwar mutumin wanda tun a ranar 22 ga watan nan yake karbar magani bayan gano alamun cutar ta Ebola tattare da shi.

Rahotanni sun bayyana cewa, tun a ranar 13 ga watan nan ne, mutumin wanda aka bayyana da mahakin zinare daga kauyen Mongbwalu na yankin Ituri mai nisan kilomita 600 daga babban birnin kasar ya isa birnin na Goma da nufin ziyarar ahalinsa, sai dai bayan kwanaki 10 a ranar 22 ga watan nan ya ziyarci asibiti bayan bayyana wasu alamomin cutar a tare da shi.

A cewar Giscard Kusema, babban jami’in yada labaran fadar shugaban kasar Congon, tun a wancan lokaci kafin tabbatar da cewa yana dauke da cutar ta Ebola a jiya Talata, aka fara bashi kulawa tare da bashi magungunan cutar baya ga daukar matakan gwaji kan ilahirin mutanen da ya yi mu’amala da su.

Rahotanni daga birnin na Goma sun bayyana cewa hatta ahalin mutumin da duk wadanda suka yi mu’amala da su an killace su don tabbatar da cewa basu yada cutar ba, haka zalika an dauki mataki bayar da rigakafin cutar a yankin da ya zauna.

Sai dai mahukuntan a kasar ta Congo sun bayyana cewa babu alaka tsakanin Limamin majamu’ar da ya mutu ranar 16 ga watan nan a yankin Butembo sanadiyyar cutar da kuma wanda ya mutun a yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.