rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An rufe makarantun Sudan saboda kashe dalibai

media
Wasu daga cikin daliban Sudan rike da tutocin kasar a zanga-zangar da suka shiga bayan kashe 'yan uwansu dalibai. Ebrahim HAMID / AFP

Hukumomin Sudan sun sanar da rufe makarantun kasar baki daya bayan da dalibai suka kaddamar da zanga-zangar adawa da kisan gillar da aka yi wa wasu masu zanga-zanga guda 6, cikin su harda 'yan makaranta guda 5.


Daruruwan daliban da suka shiga zanga-zangar gama-garin dauke da tutocin kasar, sun bayyana cewar kashe dalibi tamkar kashe kasa ne, inda suka yi jerin gwano a Khartoum da Omdurman da kuma sauran biranen kasar.

Rahotanni sun ce, dalibai 5 aka kashe yayinda sama da 60 suka samu raunuka lokacin da wasu maharba suka bude musu wuta a Al-Obeid, kisan da aka danganta shi da jamiā€™an tsaron da ke kai daukin gaggawa.

Wannan kisan ya sa shugabannin masu zanga-zangar soke shirin ganawarsu da wakilan gwamnatin soji a kokarin da suke na kammala kafa gwamnatin rikon kwaryar da za ta kama aiki.

Hukumar Kula da Ilimin Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bukaci gudanar da bincike kan kisan daliban.