rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jagoran 'yan awaren Kamaru ya kauracewa cin abinci

media
Jagoran ‘yan aware na kasar Kamaru dake tsare Julius Sisuku Ayuk Tabe. YouTube

Jagoran ‘yan aware na kasar Kamaru dake tsare Julius Sisuku Ayuk Tabe, ya kaddamar da soma yajin kin cin abinci, don rashin sanar dashi inda aka kai abokan gwagwarmayar sa da ake tsare dasu tare.


Daya daga cikin lauyoyinmsa Joseph Fru ya sanar da cewa tun daren Talata ne jagoran ‘yan awaren na yankin Ambazonia yaki cin abinci.

Kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP ya sanar da cewa yaga wasikar da Lauyan ya rubutawa Ministan Shari’a na Kamaru dake ankarar dashi cewa Ayuk Tabe ya fara yajin kin cin abinci, saboda rashin sanin inda aka yi da abokan gwagwarmayar tasa da ake tsare dasu tare.

Daruruwan ‘yan gidan kaso ne suka yi bore a baya bayan nan a gidan Yari mai cunkoso dake Yaunde da kuma wanda yake Buea.

Fursunonin da suka yi boren mafi yawa masu adawa da manufofin gwamnatin Kamaru da kuma ‘yan aware ne dake yankin masu Magana da turancin ingilishi, inda suka baza hotuna na bidiyo na irin matsanancin halin da suke cikin a tsare.