Isa ga babban shafi
Najeriya-Shi'a

Najeriya ta yi watsi da bukatar Iran kan Zakzaky

Gwamnatin Najeriya ta ki amincewa da bukatar Iran game da sakin shugaban kungiyar Shi’a Ibrahim Zakzaky don ziyartar asibiti a Tehran da nufin duba lafiyarsa.

Jagoran mabiya Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Jagoran mabiya Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Talla

Wata majiya da jaridar Punch a Najeriyar ta ruwaito ta bayyana cewa, watsi da bukatar ta Iran ya biyo bayan kin amincewar da wasu jiga-jigan gwamnatin Najeriyar suka yi, ciki har da gwamnonin yankin arewaci 11 da kuma babban sufeton ‘yan sandan kasar Mohammed Adamu.

Jaridar ta ruwaito cewa kafin gwamnati ta yi watsi da bukatar sai da aka gudanar da wani ggarumin taro a jihar Katsina wanda ya tattauna batutuwan kalubalen tsaron da Najeriyar ke fuskanta ciki har da barazanar kungiyar ta Shi’a.

Bayan karkare taron wanda aka gudanar cikin matukar sirri, jiga-jigan gwamnatin Najeriyar da babban sufeton ‘yan sandan kasar sun bayyana cewa batu ne mai matukar hadari bayar da damar fitar da jagoran na Shi’a zuwa Iran.

Majiyar ta bayyana cewa akwai yiwuwar ko da gwamnatin Najeriyar ta saki Zakzaky daga daurin kusan shekaru 3 da take masa, za a iya haramta masa balaguro zuwa ketare.

A juma’ar da ta gabata ne, babban mai shigar da kara a Iran Mohammed Montazeri ya aikewa gwamnatin Najeriyar wasikar da ke bukatar aikewa da Ibrahim Zakzaky Tehran don duba lafiyarsa, matakin da ke biyo bayan rahotanni kan yadda rashin lafiyarsa ta tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.