
Farfesa Muntaka Usman game da umarnin Kotu na daina biyan tsaffin Gwamnoni Fansho
A Nigeria Rundunar ‘yan sandan kasar ta haramta zanga-zangar juyin-juya hali da wata kungiya da wani dan siyasa, mawallafin Mujallar Sahara Reporters Omoyele Sowore ya kira ayi yau a birnin Abuja. A yanzu haka dai shi mutumin na hannun ‘yan sandan ciki ana tatsar bayanai daga gareshi.Tun bayan kama shi karshen makon daya gabata mutane da dama cikin har da Atiku Abubakar da Farfesa Wole Soyinka ke ta kiran a sako shi. Mun nemi ji daga bakin Farfesa Shehu Abdullahi Zuru masanin sharia da ke Jamiar Abuja yadda yake kallon lamarin.