Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar RevolutinNow a Lagos

A Najeriya jami’an tsaro na musamman da aka girke a jihar Lagos sun tarwatsa dandazon masu zanga-zangar juyin-juya hali da suka yiwa suna da RevlutionNow, wadanda suka taru tunda safiyar yau Litinin don nuna adawa da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Jami'an tsaron Najeriya lokacin da su ke tarwatsa masu zanga-zangar RevolutionNow a Lagos
Jami'an tsaron Najeriya lokacin da su ke tarwatsa masu zanga-zangar RevolutionNow a Lagos Naija news
Talla

Tun da sanyi safiya ne dai aka girke tarin jami’an tsaron na musamman a babban filin wasa Surulere da ke jihar ta Lagos wajen da a nan ne aka tsara haduwar masu zanga-zangar ta RovolutionNow, zanga-zangar da gwamnatin kasar ke zargin wasu tsirarun ‘yan adawa da kitsawa da nufin kara tarnaki ga kasar wadda ke fuskantar matsalolin tsaro.

Wasu ganau sun shaida yadda jami'an tsaron suka rika harba hayaki mai sanya hawaye kan dandazon masu zanga-zangar da suka hadu a wajen don fara gangamin, ko da dai kawo yanzu babu rahoton jikkata ko rasa rai a arangamar tsakanin jami'an da masu zanga-zangar da ke ikirarin kalubalantar matsalar tsaron da Najeriyar ke fuskanta.

Tun a ranar Asabar din da ta gabata Rundunar 'yan sandan Najeriyar ta gargadi masu zanga-zangar ta RevolutionNow tare da barazanar ayyana duk wanda ya shiga gangamin a matsayin dan ta'adda, baya ga daukar matakin kame jagoran zanga-zangar a daren Juma'a.

Mawallafin ‘Sahara Reporters’ Omoyele Sowore ne dai tare da wasu masu fafutukar kare hakkin jama’a suka kira gangamin a fadin Najeriya, domin nuna rashin amincewa da yadda talauci da rashin tsaro da kuma kuncin rayuwa suka yiwa al’ummar kasar dabaibayi.

A cewar wata Majiya daga jihar ta Lagos jami’an tsaron da aka jibge ba nau’in wadanda aka saba gani ba ne don bayar da tsaro a wuraren zanga-zanga, a cewar majiyar jami’ai ne na hadaka da suka kunshi Sojin Sama na ruwa da kuma na kasa dukkanninsu dauke da makamai.

Gwamnatin Najeriya ta bukaci jama’a da su kara hakuri saboda kokarin da take na shawo kan matsalolin da suka addabi kasar, amma masu shirya zanga zangar sun bukaci jama’a da su yi watsi da bukatar wajen fitowa domin nuna fushin su akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.