rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Libya Rikicin Kasar Libya Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dakarun Haftar sun kai farmaki kan filin jiragen saman Misrata

media
Wasu daga cikin dakarun Janar Khalifa Haftar a birnin Benghazi na Libya. Reuters/ Esam Omran Al-Fetori

Dakarun Janar Khalifa Haftar dake kokarin kwace iko da Tripoli babban birnin kasar Libya, sun sanar da kai hari filin jiragen saman Misrata dake karkashin ikon gwamnati, kwanaki bayan munanan hare haren da suka kai kan Tripoli da ya tilasta karkata akalar jiragen dake sauka zuwa birnin na Misrata.


Sanarwar da dakarun suka fitar tace sun yi nasarar kai hare-haren sama da dama kan filin jiragen da kuma kayayyakin sojin gwamnatin Turkiya da suka hada da makamai da jirage masu sarrafa kansu.

Tashar talabijin din Al Hadath dake goyan bayan Haftar tace sun lalata jirgin yakin Turkiya a tashar.

A karshen watan Yuni babban Hafson Sojin Libya mai karfin fada aji da ke riko da galibin yankunan kasar musamman a yankin gabashi, Khalifa Haftar ya bukaci sojojinsa, su soma kai farmaki kan jiragen ruwa da sauran kadadrorin kasar Turkiya da ke Libya, bayan zargin da ya yi na cewa Turkiya na taimawa bangaren gwamnati mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.