rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mulkin Najeriya da wahala - IBB

media
Ibrahim Babangida tsohon shugaban Nigeria REUTERS/Luc Gnago

Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce mulkin Najeriya akwai wahala.


Ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai sarkakiya da wahalar tafiyarwa saboda yanayin al’ummar ta da bambance – bambancensu.

A cewarsa, bambance – bambancen sun kawo ra’ayoyi mabambamta tare da muhawwara zafafa,wadda wani lokaci ke kaiwa ga kiyayya da tashin hankali.

Da yake jawabi a Minna ta jihar Neja a Najeriya, yayin ziyarar da wasu shugabannin marasa rinjaye na majalisar wakilan kasar karkashin jagorancin Ndudi Elumelu suka kai mai a gidansa, Babangida ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai karsashi da ban sha’awa.

Ya bukaci ‘yan siyasa da kada su karaya da sarkakiyar kasar, maimakon haka su mayar da hankali wajen ciyar da ita gaba ta wajen amfani da yanayin al’ummarta.