Isa ga babban shafi

Buhari ya yi umarnin bincike kan Sojojin da suka kashe 'yan sanda

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci shalkwatar tsaron kasar ta gudanar da bincike kan kisan wasu jami’an ‘yansanda 3 da farar hula da rundunar ‘yansandan kasar ke zargin Sojin bataliya ta 93 da ke Takum a jihar Taraba da aikatawa.

Wasu Sojin Najeriya
Wasu Sojin Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Babban Hafson Sojin saman Najeriyar, Sadique Abubakar wanda ke bayyna hakan ga manema labarai a Abuja babban birnin kasar bayan kammala taron kolin tsaro karkashin jagorancin Muhammadu Buhari, ya ce za su gudanar da gagarumin bincike tare da hukunci mai zafi matukar aka samu jami’an na su da laifi a batun.

Kamfanin Dillancin labaran Najeriyar NAN ya ruwaito cewa a jiya Laraba Rundunar Sojin kasar da ta ‘yan sanda sun kafa wani kwamitin bincike na hadin gwiwa don bibiyar lamarin.

A bangare guda mukaddashin daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriyar Sagir Musa ya bayyana cewa bangaren ‘yan sandan kasar ne za su jagoranci kwamitin binciken wanda ya sha alwashin tabbatar da adalci.

Tun a jiya Laraba ne dai rundunar 'yan Sandan Najeriyar ta zargi sojojin kasar da kashe mata jami’ai 3 baya ga raunata wasu da dama lokacin da suka kamo wani mai garkuwa da mutane akan hanyar Ibi zuwa Jalingo da ke Jihar Taraba.

Kakakin 'yan Sandan kasar Frank Mba ya ce, lamarin ya faru ne lokacin da sojojin suka bude musu wuta duk da gabatar da shaidar da ke nuna cewa, su jami’an 'yan sanda ne da ke gudanar da aikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.