rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Ebola

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Congo na tuhumar jami'an lafiyarta 3 da kashe likitan WHO

media
Wasu jami'an lafiya da ke aikin yaki da cutar Ebola a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo (WHO)

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ta tsare wasu ma’aikatan lafiya 3 bisa zargin su da kashe likitin Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO da ke yaki da cutar Ebola a kasar.


A ranar 19 ga watan Afrilun da ya gabata ne, aka harbe likitin na Hukumar Lafiyar dan asalin kasar Kamaru, wato Richard Valery Mouzoko Kiboung, a wani hari da aka kaddamar kan asibitin gabashin birnin Butembo.

Ma’aikatan Lafiyar kasar 3 da aka cafke saboda zargin su da hannu a kisan Likitan, za a tuhume su da aikata ta’addanci da kuma kitsa mummunan aiki kamar yadda mai shigar da kara na sojin kasar, Laftanar Kanar Jean Baptiste Kumbu Ngoma ya sanar.

An dai zargi mutanen 3 da gudanar da wani taron sirri a ranar 14 ga watan Afrilu, inda suka kitsa yadda za su salwantar da rayuwar likitan na Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ta tura jami’in na ta ne zuwa Jamhuriyar Congo domin shiga cikin tawagar da ke yaki da cutar Ebola wadda ta sake barkewa a cikin watan Agusta a arewacin Kivu.

Sai dai a bangare guda, Kungiyar Likitocin Cikin Gida ta bayyana bacin ranta kan cafke ‘ya’yanta, ta na mai cewa, za ta tsunduma cikin yajin aiki muddin aka gaza sako su cikin sa’o’i 48.