rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tanzania

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana zaman makoki a Tanzania don mutanen da gobarar tankar mai ta lakume

media
Hayakn daya turnike sararin sama biyo bayan gabarar tankara mai REUTERS TV

A yau Lahadi Tanzania ta shiga zaman makoki, yayin da ake jana’izar mutane 69 da suka mutu sakamakon kalar man fetur da suka je yi lokacin da wata motar dakon man da ta fadi ta yi bindiga.


Shugaba John Magufuli ya ayyana makoki daga ranar Litinin, biyo bayan wannan mummunan hatsarin da ya auku kusa da garin Mororgoro, yammacin birnin Dar es Salam.

Wata sanarwa daga fadar shugana kasar ta ce Firaminista Kassim Majaliwa zai wakilci shugaban kasar a wajen jana’izar wadda aka fara a yau.

Shugaba Magufuli ya ziyarci wadanda suka ji rauni a hatsarin a wani asibiti a birnin Dar es Salam.

Firaminista Majaliwa ya bada sanarwar cewa za a kafa wani kwamitin bincike na musamman don gano musabbabin wannan hatsari da ya lakume rayuka.