rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kano

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hawan Daushen hakimai a sabbin masarautun Kano

media
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da Maimartaba Sakin Kano Muhammadu Sanusi II. vanguard

Gwamnatin Jihar Kano a Najeriya ta umarci hakimai da su tabbatar da cewa sun halarci Hawan Daushe da aka saba yi a lokacin sallah a sabbin masarautun da aka kirkiro, maimakon zuwa birnin Kano kamar yadda suka saba a baya.


Sanarwa daga fadar gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, ta umarci illahirin hakimai da ke karkashin mulkin sabbin masarautun da aka kirkiro da suka hada da Bichi, Rano, Karaye da kuma Gaya da su yi wannan hawa a sabbin masarautun, yayin da sauran da ke karkashin tsohuwar masauratar Kano za su yi nasu hawan a Kano.

Wannan dai na kara fitowo fili da tsamin dangantaka tsakanin gwamnatin jihar ta Kano da kuma masarautar ta Kano mai dadadden tarihi.