rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

India Pakistan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An tsaurara matakan tsaro lokacin bukukuwan sallah a Kashmir

media
Masu zanga-zanga bayan da India tasokekwarya-kwaryan 'yancin cin gashin kan yankin Kashmirr Kashmir, in New Delhi, India, August 5, 2019. REUTERS/Danish Siddiqui

Yayin da ake gudanar da bukukuwan sallar Layyah a yankin Kashmir, a yau litinin mahukunta a India sun baza dimbin jami’an tsaro domin kasancewa a cikin shirin ko-ta-kwana, a daidai lokacin da ake fargabar barkewar torzoma saboda matakin da India ta dauka na soke kwarya-kwaryan ‘yancin cin gashin kan yankin da mafi yawan mazaunansa musulmai ne.


Baya ga baza dimbin jami’an tsaro, hakazalika mahukunta sun katse wayoyin sadarwa da kuma na Internet a yankin baki daya, yayin da jami’an tsaro ke sintiri a Srinagar da kuma sauran manyan birane da ke yankin na Kashmir.

To sai dai firaministan Pakistan Imran Khan, ya bayyana matakin da India ta dauka kan Kashmir a matsayin mamaye wadda ba ta da bambanci da wadda ‘yan Nazi suka yi a lokacin yakin duniya na biyu.

Khan ya ce India na fatan yin amfani da baraden matasa masu zazzafen ra’ayin kishin kasa domin afka wa mazauna yankin na Kashmir wadanda mafi yawansu musulmi ne.