rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Chadi Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yar kunar bakin wake ta kashe mutane a Chadi

media
Boko Haram na ci gaba da addabar kasashen yankin tafkin Chadi REUTERS/Moumine Ngarmbassa

Wata ‘yar kunar bakin wake ta tarwatsa kanta da bama-bamai, inda ta kashe mutane akalla shida da suka hada da jami’in soji guda a kasar Chadi, harin da aka danganta da kungiyar Boko Haram.


Majiyar sojin kasar ta tabbatar da jikkatar mutane da dama a sakamakon harin na ranar Laraba a yankin Kaiga-Kindjiria na kasar.

Kodayake kawo yanzu, Boko Haram ba ta fito karara ta dauki alhakin harin ba, amma  Chadi na daya daga cikin kasashen yankin tafkin Chadi da ke fama da hare-haren kungiyar.

Tun shekarar 2018, Boko Haram mai cibiya a Najeriya, ta kai hare-hare har guda 10 a Chadi, akasari kan jami’an tsaro.

Kungiyar dai na ci gaba da addabar kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, yayinda ta kashe akalla mutane dubu 27 tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.