Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta yi tayin karbar 'yan ci ranin da Italiya ta kora

Faransa tace a shirye take ta karbi ‘yan ci rani 40 daga cikin 107 dake makale a kan teku, bayanda kasar Italiya ta ki karbar su.

Jirgin ruwan agajin Spain na Open Arms da ya ceto 'yan ci rani daga teku, a kusa tsibirin Lampedusa, na Italiya..
Jirgin ruwan agajin Spain na Open Arms da ya ceto 'yan ci rani daga teku, a kusa tsibirin Lampedusa, na Italiya.. REUTERS/Guglielmo Mangiapane
Talla

Tayin na Faransa ya zo ne bayanda kasar Spain ta baiwa jirgin ruwan agaji na Open Arms da ya ceto ‘yan ci ranin damar isa gabar ruwanta, damar da ministan cikin gidan Italiya Matteo Salvini ya haramtawa jirgin agajin.

A ranar asabar ne dai, masu gabatar da kara a Italiya, suka soma gudanar da bincike, kan ministan cikin gidan kasar, bisa zarginsa da yin amfani da karfin iko ta hanyar da bata dace ba, bayan haramtawa jirgin ruwan agajin da ya ceto ‘yan ci rani daga teku shiga cikin kasar.

Ranar asabar, ministan cikin gidan na Italiya ya baiwa kananan yaran da basa tare da iyayensu guda 27, daga cikin ‘yan ci rani sama da 100 da aka ceto daga tekun Mediterranean damar shiga cikin kasar, inda yacesaura 107 za su ci gaba da zama a gabar tekun.

Sai dai cikin wasikar da ya aikewa ofishin Fira Ministan kasar ta Italiya, Salvini ya ce ya bada umarnin ne ba a son ransa ba, inda ya sha alwashin ragowar ‘yan ci ranin manya 105 da kuma yara biyu, za su ci gaba da zama a gabar tekun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.