rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An fara shari'ar Omar al-Bashir na Sudan

media
Toshon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir REUTERS/Umit Bektas

A yayinda aka fara yi masa shari’a kan cin hanci da rashawa, tsohon shugaban Sudan, Omar al-Bashir ya amince da karbar tsabar kudi har Dala miliyan 90 daga masarautar Saudiya.


Wani jami’in bincike mai mukamin Birgediya a rundunar ‘yan sandan kasar, Ahmed Ali ya shaida wa kotun birnin Khartoum cewa, tsohon shugaban ya fada masa cewa, ayarin Yarima mai jiran gadon Saudiya, Mohammed bin Salman ne ya kawo masa makuden kudaden.

A wannan Litinin din ne Omar al-Bashir wanda ya mulki Sudan tsawon shekaru 30 ya isa kotun, inda ake yi masa shari’a cikin cikakken tsaron jami’an sojoji.

An dai killace tsohon shugaban cikin wani akurkin karfe, sanye da dogon tufafin gargajiya, sannan kuma ba a yi masa gyaran fuska ba.

An jiyo danginsa na daga murya suna fadin “Allahu Akbar”, wato Allah Shi ne mai girma, yayinda shi ma ya yi makamanciyar wannan kabbarar.

A ranar 11 ga watan Afrilun da ya gabata ne, aka tilasta wa Bashir sauka daga madafun iko bayan ‘yan kasar sun kwashe watanni suna zanga-zanga, yayinda a ranar Asabar da ta gabata, majalisar sojin kasar da bangaren masu zanga-zangar suka cimma yarjejeniya kan tsarin mulkin da zai kai ga kafa gwamnatin farar hula a kasar.

A bangare guda, tsohon shugaban na fuskatar tarin tuhuma kan aikata laifukan yaki da cin zarafin al’umma da kisan kare dangi daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya saboda rawar da ya taka a yakin Dafur.