rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kwando Najeriya Senegal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya ta lashe kofin gasar kwallon kwandon mata

media
Tawagar kwallon kwando ta Najeriya D' Tigress, bayan lashe kofin gasar kwallon kwando ta nahiyar Afrika. Pulse/FIBA

Tawagar kwallon kwandon Najeriya D’ Tigress ta sake lashe kofin gasar kwallon kwandon Nahiyar Afrika ta mata.


Karo na biyu a jere kenan da Najeriya ke lashe gasar kwallon kwandon yayinda a jimlace ta lashe kofin sau hudu, a shekarun 2003, 2005 da kuma 2017 sai kuma na bana.

A ranar Lahadi ‘yan matan na Najeriya suka lallasa takwarorinsu na Senegal mai masaukin baki, da kwallaye 65 da kuma 55.

A shekarar 2017 ma dai an fafata wasan karshen gasar ce tsakanin kasashen biyu, inda Najeriyar ta doke Senegal da kwallaye 65 da kuma 48.

A wasannin baya da ta fafata yayin gasar, Najeriya ta lallasa Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo da kwallaye 79 da 46.

Tunisia kuwa ta sha kashi a hannun D’ Tigress ne da kwallaye 76 da 25, sai kuma Kamaru da Najeriyar ta yiwa Dukan kawo wuka da kwallaye 106 da 39.