rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Burkina Faso Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Burkina Faso

media
Wasu daga cikin sojojin Burkina Faso dauke da gawar daya daga cikin wadanda 'yan bindiga suka kashe a kwanakin baya Ahmed OUOBA / AFP

Ma’aikatar Tsaron Burkina Faso ta tabbatar da mutuwar dakarun kasar akalla 12 yayinda wasu da dama suka bata a yankin Soum da ke daf da ikyar kasar da Mali.


Sanarwar Ma’aikatar Tsaron ta ce mahara dauke da manyan makamai ne suka yi wa karamin barikin soji da ke garin Koutougou a lardin Soum kofar rago, inda suka kashe sojoji akalla 12, sannan wasu da dama suka jikkata.

Wasu majiyoyin tsaro sun ce, adadin wadanda suka rasa rayukansu ya kai sojoji 20, yayinda har zuwa yammacin ranar Litinin, akwai wani adadi na sojoji masu tarin yawa da ba a san inda suke ba.

Wannan shi ne karo na farko da Ma’aikatar Tsaron Kasar ta tabbatar da asarar sojoji masu tarin yawa a lokaci guda, bayan harin da aka kai cikin watan Disambar 2016 a wani gari mai suna Nassoumbou, inda a wancan lokacin ‘yan bindiga suka kashe dakarun kasar 12.

Mafi yawan lokuta, ‘yan ta’addar na zuwa ne a kan babura ko kuma a cikin motoci daga makociyar kasar Mali domin kai farmaki a kan sojojin da ke sintiri ko kuma barikokinsu musamman a yankin na Soum da kuma Jibo da ke daf da iyakar kasar ta Burkina Faso da Mali.