rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Sojin Kamaru za ta hukunta jagoran 'yan adawa

media
Maurice Kamto REUTERS/Zohra Bensemra

Kotun Sojin Kamaru za ta fara zaman shari’ar jagoran ‘yan adawar kasar, Maurice Kamto da aka garkame a gidan yari tun watan Janairun da ya gabata. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke caccakar matakin kotun sojin na yanke wa fararen hula hukunci a kasar.


Nan da ranar 6 ga watan Satumba mai zuwa ne, kotun sojin ta Kamaru za ta fara shari’ar kan Kamto kamar yadda lauyan jam’iyyarsa ya shaida wa Kamfanin Dillancn Labaran Faransa na AFP.

An kama Mr. Kamto ne bayan kammala zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 7 ga watan Oktoban bara, yayinda aka cafke wasu karin mutane 150 biyo bayan zanga-zangar da suka gudanar a ranar 26 ga watan Janairun wannan shekarar.

Jam’iyyar Kamto ta MRC ce ta kira wannan zanga-zangar domin nuna adawa da nasarar da shugaba Paul Biya ya sake samu a zaben na shugaban kasa.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai, kotun sojin ta bukaci Kamto da ya bayyana a gabanta, inda ta shaida masa ranar da za ta yi masa shari’a.

Sai dai lauyan jagoran ‘yan adawar, Emmanuel Simh ya ce za su daukaka kara domin kalubalantar hurumin kotun sojin na yi wa fararen hula hukunci.

A bangare guda, a farkon makon nan ne, kotun sojin ta Kamaru ta yi wa jagoran ‘yan awaren kasar , Julius Ayuk Tabe da wasu mukarrabansa daurin rai da rai bayan ta same su da laifin raba kan al’ummar kasar ta hanyar yunkurin ballewa domin kafa kasar Ambazonia.