rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Somalia Habasha Kenya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan takarar yankin Jubaland sun yi ikirarin nasarar lashe zabe

media
Shugaban yankin Jubaland na Somalia mai ci Ahmed Madobe, da yayi ikirarin lashe zabe tare da babbar abokiyar hamayyarsa Anab Mohamed Dahir. AFP/Abdirazak Hussein FARAH

Yan takara biyu dake hamayya da juna a Smalia, sun yi ikirarin lashe zaben yankin Jubaland dake kudancin kasar mai amfana da wani mataki na kwarya-kwaryar cin kashin kai.


Tuni dai gwamnatin kasar ta Somalia dake Mogadishu ta bayyana rashin amincewa da sakamakon zaben.

An dai yi ta dage zaben fidda shugaban yankin na Jubaland, dake da iyaka da kasar Kenya, sakamakon abin da masu sa ido suka daganta da gwagwarmayar karbe iko tsakanin yankin da kuma gwamnatin tsakiya ta Mogadishu.

Mahukuntan yankin Jubaland sun zargi gwamnatin Somalia da fadada ikonta na tsige shugaba Ahmed Madobe da sauya shi da wanda da ke yi mata biyayya.

A halin dake ciki, rahotanni sun ce rikici kan zaben na barazanar bazuwa zuwa sassan yankin na Jubaland da makwabtansa, inda kasar Kenya ke marawa Madobe baya yayin da Habasha ke bayan Mogadishu mai kokarin kawar da Madobe daga kujerar mulki

Sakamakon zaben yankin dai ya nuna cewar Madobe tsohon madugun yan tawaye, ya lashe kuri'u 56 cikin 74 da ‘yan majalisar yankin na Jubaland suka jefa wanda zai tabbatar da shi shugaba na tsawon shekaru 4; yayinda Anab Mohamed Dahir, babbar abokiyar hamayyarsa kuma mace daya tilo da ta tsaya takara shi, ta samu kuri'u 17.