rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

‘Yan gudun Hijira Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan cirani 356 za su samu matsugunai a kassahen EU 6

media
Wasu tarin 'yan cirani da aka yi nasarar cetowa REUTERS/Guglielmo Mangiapane

Wasu kasashen kungiyar Tarayyar Turai 6 sun amince da karbar ‘yan cirani 356 wadanda jirgin ruwan Ocean Viking mallakin kasar Norway ya ceto a tekun mediterranean karkashin jagorancin kungiyoyin agaji na MSF da SOS.


Rahotanni sun bayyana cewa tsakankanin ranakun 9 zuwa 12 ga watan nan ne, kungiyoyin agajin biyu suka yi nasarar ceto ‘yan ciranin daga kananun jirage 4 lokacin da suke kokarin tsallakawa nahiyar Turai ta tsakiyar tekun Mediterranean daga Libya.

Kassahen da suka amince da karbar ‘yan ciranin sun hada da Faransa da Jamus da Ireland da Luxembourg da kuma Portugal baya ga Romania.