rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sudan na bukatar tallafin dala biliyan 8 - Hamdok

media
Fira ministan Sudan Abdalla Hamdok. Ebrahim HAMID / AFP

Sabon Fira Ministan Sudan, Abdalla Hamdok, ya ce suna bukatar tallafin akalla dala biliyan 8 daga kasashen duniya, domin sake gina tattalin arzikin kasar da ya durkushe, bayan shafe watanni cikin rikicin siyasar da ya kawo karshen mulkin tsohon shugaba Oumar Al-Bashir da kuma shugabancin gwamnatin soji zalla.


Fira Ministan ya kuma ce Sudan na bukatar tallafin Karin dala biliyan 2 na dabam, cikin watanni uku masu zuwa, domin farfado da asusun ajiyarta na kasashen ketare.

Ranar Alhamis aka rantsar da Hamdok, tsohon babban jamiā€™in majalisar dinkin duniya, a matsayin shugaban sabuwar gwamnatin Sudan ta hadakar soji da farar hula.

A watan Afrilun da ya gabata, zanga-zangar gama gari kan matsin tattalin arzikin da ya kunshi karancin abinci, man fetur da kuma kudaden ketare, ta tilastawa tsohon shugaban Sudan Oumar Al Bashir rasa kujerarsa, bayan da sojoji suka karbe mulki.